OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya Na Barazanar Mamaye Ma'aikatar Ilimi

Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya Na Barazanar Mamaye Ma'aikatar I

NANS Logo: Pilot News

Shugaban tsagin kungiyar daliban Najeriya Farouk Lawal a ranar Alhamis ya yi barazanar mamaye harabar ma’aikatar ilimi ta tarayya.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, Lawal ya bayyana cewa kungiyar daliban za ta kuma samar da wani tsari na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a manyan makarantun Najeriya.

“Muna baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adi, Za mu zaburar da dalibai domin su mamaye ma’aikatar ilimi har sai an biya mana bukatun mu.

“Muna kuma kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa kwamitoci domin gudanar da bincike kan duk wani dalibin da aka kora a siyasance da kuma ‘yan bangar siyasa.

“Muna kuma son duk masu ruwa da tsaki a harkar ilimi su tabbatar sun tsunduma ciki don ganin an tabbatar da baiwa ilimi kulawar da ake bukata ta hanyar kara wa ma’aikatar ilimi kasafin kudin."

Da yake nasa jawabin, wani ɗan ƙungiyar Adediwura Adeshina, ya bayyana cewa kungiyar za ta gana da shugabannin dalibai a fadin kasar nan domin tabbatar da an yi shiri dangane da gudanar da zanga-zangar, cewar Jaridar Punch.

“A matsayi na na Shugaban Majalisar Dattawa na kungiyar, za mu kuma yi aiki tare da dukkan shugabannin kungiyoyin daliban da ke fadin kasar nan.

"Ba za mu iya ba ku ranar ba tukunna amma za ku iya kasancewa da tabbaci cewa za mu hadu kuma za mu mamaye ma'aikatar."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci