OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Tuɓaɓɓen Sarkin Zamfara Ya Rasu A Dubai

Tuɓaɓɓen Sarkin Zamfara Ya Rasu A Dubai

Photo Source: Blueprint

Tsohon Sarkin Zurmi na jihar Zamfara Abubakar Atiku ya rasu a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Atiku ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke birnin Abu Dhabi bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Wani dan uwansa mai suna Sani Zurmi ya shaidawa jaridar Punch cewa har yanzu ba's dawo da gawar mamacin Najeriya domin binne shi ba.

"Har yanzu gawarsa tana Dubai saboda rashin samun hali don dawo da marigayin gida don binne shi". Inji Zurmi.

In baku mantaba an ruwaito cewa an tsige marigayin ne tare da Sarkin Ɗan Sadau, Husaini Umar a ranar 27 ga Afrilu, 2021, bisa zargin taimakawa ‘yan fashi a masarautun su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci