OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Tallafin kudin mai:'Yan majalisar Wakilai sun fara tantance yawan man da ake amfani da shi a kullum a Najeriya

Tallafin kudin mai:'Yan majalisar Wakilai sun fara tantance

Kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai kan harkokin da suka shafi amfani da man fetur sun fara tantance yawan man fetur din da ake amfani da shi a kullum.

Shugaban kwamitin, Uzoma Abonta,wanda ya jagoranci sauran mambobin kwamitin a ziyarar gani da ido da su ka kai gidajen mai da ke garin Calaba.

George Ene-Ita, kodinetan na, Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority, ofishin shiyyar Kudu shi ne ya jagoranci zagayen gonakin.

Mista Abonta ya ce bisa la’akari da muhawarar da ake yi kan ko ya kamata a cire tallafin man fetur ko a’a, majalisar wakilai ta kafa kwamitin da zai yi dubi da yadda ake amfani da mai a kasar.

A cewarsa rahoton kwamitin majalisa za ta yi amfani da shi a matsayin sheda domin kamala batutuwan da suka shafi tallafin.

"Muna kokarin gano yawan mai da ake amfani da sh a kasar a kullum. Majalisar wakilai za ta yi amfani da wannan rahoto a matsayin sheda don kammala wasu bincike.

Tallafin ya zama batun da ya dade yana ciwa 'yan Najeriya tuwo a kwarya sai dai ba za a iya samun asalin kididdigar lissafin tallafin ba tare da sanin ainihin yawan shi ba.

“A karshen atisayen, idan mun sami lissafin daidai, Majalisar Wakilai ita ya dace ta jagoranci wannan batu tare da dubi akan tallafin yadda ya kamata ko kuma ta yi wani abu.

"An yi ta cece-kuce kan batun tallafi; musamman kan wanda ya biya , wanda ya samu da kuma daraja” ya kara da cewa.

Wasu daga cikin gidajen man da aka ziyarta sun hada da, Northwest Petroleum, Ammasco Petrochemicals Company, Mainland Oil and Gas, Alkanes, Sobaz, Ibafon da Blokks.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci