OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda Da Dama A Zamfara da Sokoto

Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda Da Dama A Zamfara da Sokot

Hoto Daga: PremiumTimes

A wani harin da sojin Najeriya suka kai maboyar kasurgumin dan ta'addan nan, Bello Turji, anyi nasarar kashe yaran sa da dama.

Harin da aka kai ta jiragen yaki da kuma ta kasa a dazukan Zamfara da Sokoto ya samar da nasara ga rundunar.

Rahotanni sun nuna cewa shahararren shugaban 'yan ta'addan, Bello Turji ya samu raunuka da dama lokacin da sojojin suka far musu.

Bayanai daga majiyoyin sojin sun nuna cewa an kai farmakin ne cikin hadin gwiwan Rundunar Sojin Sama da Operation Hadarin Daji.

Bayan harin da aka kai ta sama, an kashe 'yan ta'addan da dama sannan wadanda suka tsere kuma suka hadu da sojin kasa da suka yi musu kwanton bauna.

Har yanzu dai ba'a san adadin 'yan ta'addan da aka kashe ba.

Wata babbar majiyar soji ta ce ayyukan hadin gwiwa da sojojin sama da na kasa ke yi na samun sakamako mai kyau.

Majiyar ta ce, wani babban kwamandan rundunar sojin ne ya jagoranci sojoji zuwa sansanonin ‘yan ta'addan a jihohin Sokoto da Zamfara.

Haka kuma a lokaci guda an kai musu wasu hare-hare ta sama da jiragen yaki wanda hakan ya ba sojojin nasara.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci