OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Mun Shirya Zanga-Zangar Cire Tallafin Man Fetur— NLC,TUC

Mun Shirya Zanga-Zangar Cire Tallafin Man Fetur— NLC,TUC

NLC

Kungiyoyin Kwadago ta NLC da TUC a Kano sun ce suna ci gaba da tattara kan ‘ya’yan kungiyoyin gabanin shirin yajin aikin gama garin da ake shirin yi don nuna rashin amincewa da cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ke shirin yi.

Da yake jawabi ga mambobin majalisar jihar a ranar Laraba, shugaban kungiyar NLC, Kwamared Kabiru Ado Minjibir ya bayyana cewa suna cikin shirin gudanar da gagarumin zanga-zangar da za’a gudanar  gudanarwa a ranar 27 ga watan Janairu, 2022 kamar yada uwar kungiyar ta bada umarci.

Ya tabbatar da cewa sun dauki matakin da zai hana ‘yan daba shiga rigar zanga-zangar su tada tarzoma.

Kwamared Minjibir wanda ya koka dkan yadda gwamnati ba ta iya cika manufofi da shirye-shirye n ci gaban ma’aiakata, ya ce tabbatar da cewa ‘yan kasar nan za su bi duk wata halastacciyar hanya wajen hana cire tallafin man fetur din.

A nasa jawabin, Shugaban TUC a Kano, Kwamared Mansur Isa Adamu, ya ce ’yan kasuwa masu zaman kansu sun shirya tsaf domin hada kan ‘yan kungiyar da NLC domin nuna kin amincewa da  shirin Gwamnatin Tarayya na cire tallafin.

A baya bayan nan ne dai Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na cire tallafin man fetur tare da maye gurbinsu da alawus alawus din sufuri na wani dan lokaci don ragewa ‘yan Najeriya zafin mawuyacin halin da cire tallafin zai jefa su.

Sai dai shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan  ranar Talata ya bayyana cewa shugaba Buhari bai taba bawa kowa umarnin cire tallafin man fetur a kasar ba.

Da yake tsokaci kan hakan a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu, 2020, ministan yada labarai da al’adu, Lai Muhammad ya ce zai tuntubi ma’aikatun da suka dace da sauran masu ruwa da tsaki kafin ya yi Karin haske kan lamarin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci