OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

El-Rufa'i Ya Amince Da Uba Sani A Matsayin Gwamnan Kaduna, Dattijo Dan Majalisar Dattawa

El-Rufa'i Ya Amince Da Uba Sani A Matsayin Gwamnan Kaduna, D

Governor Nasir El-Rufa'i of Kaduna state| Photo Source: PM News

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya amince da Sanata Uba Sani a matsayin dan takarar gwamna a jam'iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.

El-Rufa'i ya yanke wannan shawarar ne bayan ganawa da wasu masu neman tsayawa takarar na jam'iyyar APC a jihar Kaduna.

An yi ta rade-radin cewa gwamnan ya aminta da tsohon shugaban ma’aikatan sa, Muhammad Sani Abdullahi wanda aka fi sani da Dattijo a matsayin dan takarar gwamnan.

Sai dai matakin da gwamnan ya dauka ya saba wa jita-jitar da ake yadawa.

A halin da ake ciki kuma El-Rufa’i ya bukaci Dattijo da ya karbi fom din tsayawa takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Dattijo ya kuma taba rike mukamin kwamishinan kasafi da tsare-tsare na gwamnatin jihar Kaduna har sau biyu.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa Dattijo ya kuma amince da matakin da gwamnan ya dauka cikin nasara.

Ya ce zai yi kokarin ganin ya kawo wa jam’iyyar APC ta Kaduna nasara a zaben 2023 mai zuwa.

A cewar majiyar, "Dattijo ya amsa a matsayin nufin Allah (SWT), yana mai biyayya ga gwamna da bangaren."

Haka kuma, kafin faruwar haka, Dattijo ya dauki fom din tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar a ranar Laraba.

Sai dai kuma nan ba da dadewa ba zai karbi fom din takarar Sanata bisa biyayya ga ubangidansa, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci