OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Limaman Bauchi Sun Yi Kiran Zarcewar Bala Mohammed A Mulki

Limaman Bauchi Sun Yi Kiran Zarcewar Bala Mohammed A Mulki

Bauchi state governor, Bala Mohammed| Photo Source: BBC

Kungiyar Limamai da Masu Wa’azin Jihar Bauchi sun nuna goyon bayan su na zarcewar Gwamna Bala Mohammed a matsayin Gwamnan Jihar Bauchi.

Kungiyar ta bayyana cewa duk da suna goyon bayan wa’adin sa na 2 don ci gaban jihar, wata rana za su so ganin ya hau kujerar shugabancin kasan nan.

Haka kuma sun yi nuni da cewa an bar jihar Bauchi a baya wajen cigaba a tsakanin takwarorin ta kafin zuwan Bala.

Shugaban kungiyar Malam Mubarak Mato Baba-Karami ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Litinin a Bauchi.

Baba-Karami ya ci gaba da cewa, a yayin da kungiyar ke yi wa Gwamna Bala addu’a, kungiyar ta san cewa mutane da dama sun nuna goyon bayan su ga Bala ya shugabanci kasa a zaben 2023.

Ya kuma yaba wa gwamnan bisa yadda ya inganta fannin lafiya, noma, ilimi da sauran ababen more rayuwa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci