OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnan Bauchi Ya Koka Akan Jirgin Helikwafta Da Ba A Sani Ba A Dajin Jihar

Gwamnan Bauchi Ya Koka Akan Jirgin Helikwafta Da Ba A Sani B

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed| Hoto Daga: BBC

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya koka kan wani jirgin sama mai saukar ungulu da aka gani a dajin Lame-Burra na jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin kwamandan Rundunar musamman ta Sojin Saman Najeriya, Air Vice Marshal Tajuddeen Yusuf wanda aka tura jihar kwanan nan.

Ya kuma bayyana cewa an tattara bayanan ne daga rahoton sirri na jami’an tsaro da sauran al’umma.

Ya bayyana cewa, yawaitan zirgazirgan Jirgin ne ya jawo shakku wanda jami'an tsaro suka fara bincike akai.

A yayin da ya bukaci rundunar sojin saman Najeriya da ta kara sanya ido, ya ce ya zama wajibi a dauki mataki kan duk wani abu da ka iya zama barazana ga al’ummar sa.

A nasa jawabin Air Vice Marshal Tajuddeen Yusuf ya ce rundunar ta himmatu wajen tabbatar da tsaron jihar yayin da ake ci gaba da bincike.

Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da baiwa rundunar sojin sama goyon baya don ganin an samu tsaro mai inganci a Jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai