OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Katsina: Akeredolu Ya Caccaki Fadar Shugaban Ƙasa Kan Bada Izinin Mallakar Bindiga

Katsina: Akeredolu Ya Caccaki Fadar Shugaban Ƙasa Kan Bada

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, ya caccaki fadar shugaban kasa kan musanta cewa ta baiwa jami’an tsaron jihar Katsina izinin dauƙar makamai.

Gwamnan ya tuhumi ba wa jami’an tsaro na Kasina izini, yayin da aka hana sauran jami’an tsaron jihohi daukar makamai.

Sai dai gwamnatin tarayyar ta musanta, inda take cewa babu wata jiha a ƙasar da ke da damar ko izinin daukar makamai.

Akeredolu, a martanin sa ga fadar shugaban kasa ya ce: “Dalilan da aka bayar na ci gaba da kin amincewa da amfani da nagartattun makamai da ₦

1jami’an tsaron jihohi ke yi abun takaici ne yayin da ake fuskantar kalubalen tsaro"

Gwamnan, a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Richard Olatunde, ya fitar, ya ce: “Tabbatar wa da Garba Shehu ya yi kan amfani da makamai da jami’an sa kai na jihar ke yi bai dace ba.

“Kokarin da ya yi na tabbatar da amfani da bindigar AK47 da ƴan banga na Jihar Katsina suka yi don samun horon ya saɓa da hankali.

"Rahoton da gidan talabijin na TVC News ya nuna cewa ƴan banga na jihar Katsina sun samu horo da AK47.

 “Wannan makami daya ne da aka ƙi amincewa da amfani dashi wa jami'an Amotekun da sauran jami'an Tsaro na Jihohi.

“Abin shakku ne cewa Garba Shehu ya zaɓi kansa a matsayin kakakin gwamnatin jihar Katsina. 

Yayin da gwamnatin jihar Katsina ba ta fito fili ta musanta maganar da Gwamna Akeredolu ya yi kan amfani da AK47 da ‘yan banga na jihar Katsina suka yi a lokacin horo, cewar Jaridar Vanguard.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci