OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Karancin Man Fetur: Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Ta Bukaci a Binciki 'Yan Kasuwa

Karancin Man Fetur: Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Ta Bukaci

Sakamokon dogayen layuka a gidajen man fetur dake garin Bauchi wanda karancin man fetur ya jawo, Majalisar dokokin jihar ta nuna damuwarta.

Yayin wani zama da majalisar ta yi a garin Bauchin, mamba mai wakiltar mazabar Katagum, Mukhtar A Suleiman, ya yi kira ga majalisar ta kawo daukin gaggawa ga jama'a.

Ya ce karancin man ya jefa jama'a cikin wahalhalu.

Ya jawo hakalin majalisar cewa yadda Ake fama da matsalar tsaro, bai kamata a bar gidajen mai cike ba.

Mataimakin kakakin majalisar, Danlami Ahmed Kawule ne ya jagoranci zaman.

Majalisar tayi kira ga gwamnatin jihar da ta zauna da dukkanin dillalan man fetur a jihar domin gano ainihin dalilan da suka jawo karancin man.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci