OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kai Mai Haɗama Ne, Marar Godiya, Wike Ya Chacchaki Ayu

Kai Mai Haɗama Ne, Marar Godiya, Wike Ya Chacchaki Ayu

Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya bayyana shugaban jam'iyyar adawa ta PDP na kasa Iyorchia Ayu a matsayin mai butulci.

Wike ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga kalaman Ayu wanda ya bayyana wadanda ke kiran ya yi murabus a matsayin yaran da ba su san lokacin da aka kafa jam’iyyar ba.

“Ban taka wata doka ba;  a gaskiya ina kokarin kawo gyara a jam’iyyar.

“A gaskiya ban damu da rigimar ba, lokacin da muka fara PDP, yaran nan a ina suke.

“Yaran ne da ba su san dalilin da ya sa muka kafa jam’iyyar ba, ba za mu bari wani mutum ya tada hankalin jam’iyyar mu ba,” inji Ayu.

Wike ya maida wannan martani ne a wajen kaddamar da aikin titi a Omerelu da ke karamar hukumar Ikwerre a jihar Ribas, cewar jaridar Daily Trust.

Ya siffanta Ayu a matsayin mutum mai kwadayi wanda ya ke neman biyan bukatar kansa kawai.”

"Kuna iya tunanin abin da mulki zai iya yi, Kuna iya tunanin rashin godiya;  yadda mutane za su iya zama masu butulci a rayuwarsu.

“Na yi tunani a matsayin shi na shugaban jam’iyya mai son cin zabe, abunda yakama ta  ita ce ya kawo zaman lafiya a jam’iyyar, ba raba kan jam’iyyar ba, bai kamata ya nuna girman kai ga jam’iyyar ba.

“Eh, yaran ne suka kawo ku, ku zama shugaban jam’iyyar, Yaran su suka kawo shi daga rafi don su maida shi shugaba.

“Ayu, an tsige shi a matsayin shugaban majalisar dattawa, kuma Obasanjo ne ya kore shi a gwamnatinsa.

"Girman kai ba zai iya kai ka ko'ina ba, yanzu mun ga ba ku son jam'iyyar ta ci zabe, za mu taimaka muku."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci