OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jigajigan APC a Kwara sun koka akan jerin sunayen majalisar yakin neman zaben Tinubu

Jigajigan APC a Kwara sun koka akan jerin sunayen  majalisar

APC

Jigajigan jam’iyyar APC a jihar Kwara ta Kudu sun bayyana rashin jin dadin su kan cire sunayen mambobin shiyyar daga cikin majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar.

Wani dattijo kuma babban sakataren kungiyar tuntuba ta jihar Kwara ta kudu (KSCF), Adebayo Daramola ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a wata sanarwa.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ta ruwaito, Daramola ya bayyana cirewan a matsayin cin mutunci ga hazakar ‘ya’yan jam’iyyar APC na shiyyar.

Ya kuma bayyana cewa shiyyar ta sadaukar da kanta ga jam’iyyar.

Mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar da aka sanya sunayen su daga jihar Kwara sun hada da: Gwamna Abdulrahman Abdulrasaq, La’Aziz Jimoh, Mista Issa Aremu da Mista Issa Onilu.

Sauran sun hada da Mista Rahman Giwa, Sen Gbemisola Saraki, Sen Ibrahim Oloriegbe Ishiaq Modibbo Kawu da Baba Rasaq, kanin Gwamnan.

A cewar Daramola: “Kada mu bar ɓarkewar da ke tafe domin tsoronmu shi ne idan Sen Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ya ci nasara, ina fatan ba za mu fuskanci irin wannan naɗin ba a nan gaba.”

Ya kuma koka da cewa duk sunayen da aka hada daga jihar sun fito ne daga shiyyar Kwara ta tsakiya, ya kara da cewa dole ne shugabannin jam’iyyar su bi musu damuwar su.

Yayin da ya ke zargin an mayar da su saniyar ware, ya ce hakan zai shafi hadin kan jam’iyyar a jihar.

Yayin da ya ke bayyana cewa shiyyar tana da kwararrun mutanen da za su hada kai domin kawo wa jam’iyyar nasara gabanin zaben 2023, ya yi kira ga gwamnan da ya gaggauta sa baki.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci