OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar Hisban Jihar Jigawa Ta Kama Wasu Mutum 31 Bisa Zargin Aikata Badala

Hukumar Hisban Jihar Jigawa Ta Kama Wasu Mutum 31 Bisa Zargi

Hisba operatives

Kungiyar Hisbah a jihar Jigawa ta kama mutane 31 da suka hada da mata 25 a karamar hukumar Kazaure da ke jihar a ranar Laraba bisa zarginsu da aikata laifukan badala.

 

Kwamandan Hisbah a jihar, Ibrahim Dahiru, ya ce an kama wadanda ake zargin ne da misalin karfe 6 na safe bisa zarginsu da yin karuwanci da shan barasa.

 

Ya shaida wa manema labarai a Dutse ranar Laraba cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani samame da hukumar Hisbah ta kai mai taken: Ka girba abin da ka shuka.

​​​​​

Kwamandan ya ce an kama kwalabe 55 na barasa da kuma lita 50 na barasa hadin gida wanda akafi sani daBurukutu’’ yayin farmaki.

​​​​

Ya ce an mika wadanda ake zargin da kayayyakin da aka kama ga hukumaryan sanda domin daukar mataki.

​​​​​​

Dahiru ya yabawa mazauna jihar bisa goyon bayan da suke baiwa hukumar Hisbah wajen gudanar da ayyukanta.

 

Ya kuma bayar da tabbacin cewa Hisbah za ta ci gaba da yaki da munanan dabiu a duk sassan jihar.

 

NAN

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci