OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Jihar Zamfara ta Rattaba Hannu Kan Dokar Hukuncin Kisa

Gwamnatin Jihar Zamfara ta Rattaba Hannu Kan Dokar Hukuncin

Gwamnatin Jihar Zamfara ta rattaba hannu kan dokar hukuncin kisa Glga ƴan ta'adda da masu basu byanan sirri a fadin jihar.

Gwamna Bello Matawalle ya sa hannu kan dokar da ta bawa kotu damar yanke hukunci kisa kan duk wanda aka kama da laifukan ta'addanci,  wandan da suka hada da, garkuwa da mutane don neman kudin fansa, kisa domin yin asiri, da bada bayannan sirri ga yan fashi.

A yayin sa hannu kan dokar, gwamna Matawalle ya ce, ya zama wajibi gwamnati ta sa hannun kan dokar lura da yadda laifuka iri-iri na jin zarafin al'umma da kashe-kashe sukayi kamari a jihar, ya kara da cewa, sabuwar dokar da gwamnatin sa ta kaddamar wata hanya ce ta samar da tsaro da rage ayyukan bata gari a Zamafara.

Al'amuran tsaro sun jima da tabarbarewa a wasu jihohi dake arewacin kasar nan, wanda suka hada Zamafara, Sokoto, Kaduna, da Katsina tun baya hare-hare da yan ta'adda suka addabi yanku nan. Inda gwamnatoci a matakin tarayya da jihohi ke daukar matakai daban-daban don ganin sun kawo karshen matsalar a yankunan su. 

Daya daga cikin manya matakai na baya bayan nan da aka dauka don magance matsalar tsaro shine na dokar hukunci kisa da Gwamna Bello Matawalle ya sawa a hannu don fara aiki a jihar Zamfara. Kamar yadda ya bayyana a yayin jawabin sa.

"A ranar ashirin da takwas (28) ga watan Yuni na shekarar da mu ke ciki, na amince da makanciyar doka wacce ke hanawa tare da hukunta duk mtutm da aka kama da yin ayyukan ta'addanci a jihar Zamfara.

"A wannan karo ma, gwamnati ta kara jaddada karin doka dake sahalewa kotu damar yan hukunci kisa ga duk wanda aka samu da laifukan satar mutum don karbar kudinfama, fashi, kisa domin aiwatar da ayyukan asiri da bada bayanan sirri ga yan ta'adda. 

"Sannan dokar ta halas ta hukuncin shekaru goma (10) zuwa ashiri (20) ga wanda aka kama da hannu wajen gudanar da ayyukan ta'addanci. 

 

 

Source: Vanguard 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci