OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Majalisar Dokokin Kano Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Ambaliyar Ruwa A Kantin Kwari

Majalisar Dokokin Kano Ta Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Ambal

Unguwanni da kasuwannin Kano sun cika maƙil da ruwa sakamakon mamakon ruwan da aka kwana ana yi

Majalisar dokokin Kano ta sanar da kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan ambaliyar ruwa a Kantin kwari.

Mamakon ruwan da aka kwana ana yi a jihar ya malale shaguna da titunan shiga kasuwar.

A zaman ta na yau, majalisar dokokin ta ce kwamitin zai binciki rugujewar gidaje da ake samu a wasu daga cikin kasuwanni da yanku nan jihar nan baki daya.

Tunda fari dai dan majalisa mai wakiltar Fagge Muhammad Tukur ne ya gabatar da kudurin dake neman majalisar tayi bincike kan musababin ambaliyar ruwan da kasuwar Kantin Kwari, ke fuskanta a damunar bana tare da tallafawa wadanda iftila'in ya shafa.

Sai dai bayan tattaunawa da akayi majalisa ta amince kudurin ya hada da sauran kasuwanni da guraren da ambaliyar ruwan ta shafa a ciki da wajen kananan hukumomin jihar nan.

Tuni dai majalisar ta baiwa shugaban kwamitin bada agajin gaggawa na majalisar ya jagoranci kwamitin ayyuka dana muhalli tare da gabatar da rahoton su nan da makwanni biyu domin daukar mataki akai.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci