OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Buhari Ya Kaddamar Da Rukunin Malamai a Borno

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da rukunin malamai da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya gina a Maiduguri.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau kamar yadda aka bawa AllNews Hausa a ranar Alhamis.

Gusau ya ce: “Babban ginin, wanda daya ne daga cikin manyan ayyuka sama da 600 da Zulum ya gabatar, an gina shi ne a Bulumkutu, kan titin filin jirgin sama."

Shugaban ya isa rukununin ne da misalin karfe 12 da kadan na rana tare da Gwamna Zulum, da mataimakinsa Umar Usman Kadafur, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, da wasu 'yan majalisar wakilai ta kasa daga jihar Borno, ministar harkokin jin kai, agajin bala'i da ci gaban jama'a, Sadiya Umar Farouq, manajan Darakta na Hukumar Raya Arewa maso Gabas, da sauran manyan jami’an gwamnati.

A cewar sanarwar: “Shugaban da ya ziyarci Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El Kanemi, ya je Maiduguri ne domin tunawa da ranar jin kai ta duniya na shekarar 2022 da ma’aikatar jin kai da ci gaban bala’o’i da ci gaban jama’a ta tarayya ta shirya.

“Ana sa ran Buhari zai kaddamar da rabon abinci na musamman ga iyalan da rikicin Boko Haram ya raba su da muhallan su, yayin da kuma zai kaddamar da matsuguni 500 ga ‘yan gudun hijirar da gwamnatin tarayya ta gina a Molai da ke wajen birnin Maiduguri.

"Gidan na daga cikin gidaje 10,000 na sake tsugunar da jama'a da shugaba Buhari ya amince da su a shekarar 2021, wanda kawo yanzu an kammala sama da gidaje 6,000."

Ku tuna cewa shugaban ya ziyarci jihar Borno sau uku tun daga shekarar 2021.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci