OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Babu Wani Tubabben Dan Bindiga Sai Wanda Ya Mutu, Cewar El-Rufa'i

Babu Wani Tubabben Dan Bindiga Sai Wanda Ya Mutu, Cewar El-R

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i| Hoto Daga: BBC

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya yi fatali da ra'ayin kiran 'yan bindiga da suka mika wuya a matsayin tubabbu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata jim kadan bayan ganawar sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

El-Rufa'i ya gana da shugaban kasar kan kisan mutane kusan 40 da aka yi a jihar a karshen mako.

Da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnati, El-Rufa’i ya ki amincewa da kiran su tubabbun ‘yan bindiga.

Ya ce, “Babu wani abu kamar tubabbun ‘yan ta’adda. Tubabbe dai shi ne wanda ya mutu. Burin mu a jihar shi ne mu kashe su (’yan ta’adda) a bar su su hadu da Allah.”

Ya kuma bayyana jin dadin sa da hukuncin da kotu ta yanke na haramta ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, inda ya kara da cewa hakan ya kara wa sojoji karfin gwiwa wajen yakar ‘yan ta’addan.

Gwamnan tare da kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar sa, Samuel Aruwan, ya ce ziyarar da ya kai wa shugaban kasar ita ce neman tallafi da kuma tura karin sojoji domin kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda.

Ya kuma kara da cewa sojoji suna sane da inda ‘yan ta’addan suke amma suna yin taka-tsan-tsan da barnar da za ta iya yi wa fararen hula.

El-Rufa’i ya kuma bukaci jami’an tsaro da su zage damtse wajen tunkarar ‘yan ta’addan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci