OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU Ta Shirya Daukaka Kara Bayan Hukuncin Kotu Dake Umartar Malamai Da Komawa Bakin Aiki

ASUU Ta Shirya Daukaka Kara Bayan Hukuncin Kotu Dake Umartar

Wasu daliban Najeriya yayin da suke zanga zangar kawo karshen yakin aikin ASUU

Kungiyar malaman jami’oi ta kasa ASUU ta sha alwashin daukaka kara game da hukuncin kotun da'ar ma'aikata da ya umarci malaman Jami'a su koma bakin aiki.

Shugaban ASUU na shiyyar jihar Lagos, Adelaja Odukoya, a wata sanarwa da ya fitar bayan kotu ta yanke hukuncin jiya, ya roki mambobin kungiyar su kwantar da hankulansu, kuma su daura damarar yaki har karshe. 

A jiya Laraba kotun ma’aikata ta bayar da umarni ga ASUU, kan ta janye yajin aikin da take yi ba tare da bata lokaci ba, bayan da gwamnatin tarayya ta gurfanar da kungiyar a kotun kan bukatar tilastawa malaman komawa bakin aiki, bayan da bangarorin biyu suka gaza cimma matsaya domin kawo karshen yajin aikin.

Tuni dai dalibai suka bayyana farin ciki kan hukuncin kotun.

Sai dai ita kungiyar ta ASUU ta ce yanzu haka ta fara tattara lauyoyi bisa jagorancin lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Femi Falana, domin shigar da kara a gaba.

Tun ranar 14 ga watan Fabarairun 2022 kungiyar malaman jami'o'i ta kasa, ASUU ta fara yajin aikin sai baba ta gani sakamakon kin biya musu wasu buƙatu da gwamnatin tarayya da amincewa a baya.

Cikin abubuwan da ASUUn ke bukata akwai biyan malaman jami'o'i ta manhajar da suka amince da shi ba IPPIS ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci