OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

ASUU: Kungiyar Iyaye Da Malamai Sun Yi Kiran Bayar Da Tallafin Kudi Ga Jami'o'i

ASUU: Kungiyar Iyaye Da Malamai Sun Yi Kiran Bayar Da Tallaf

Kungiyar iyaye da malamai ta kasa ta nemi gwamnatin tarayya da ta yi kokari don ganin an janye yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ke yi.

Kungiyar ta kuma bayar da shawarar biyan N10,000 a kowane shekara ga kowane mamba don taimakawa gwamnati wajen samar da karin kudade ga jami'o'i.

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar NAPTAN, Dokta Ademola Ekundayo, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar Punch a ranar Talata.

Dokta Ekundayo, wanda ya koka da yadda ake ci gaba da rufe jami’o’in kasar nan, ya ce iyaye suna kan gaba wajen rashin jin dadi gameda abunda da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU.

“Mun mika takarda ga ofishin Ministan Ilimi, muna neman a bamu dama inda muke fatan tattaunawa kan wata shawara, in ji shi.

“Zamu ba da gudumawar Naira 10,000 ga kowane iyaye kowane shekara da za a biya kai tsaye ga jami’o’i.  

"Wannan zai zama namu gudunmawar baya ga sauran kudaden da doka ta kayyade wajen samar da karin kudade ga jami'o'i.

“Ana iya kiransa harajin tallafin iyaye ga jami’o’i.  Mun kasance wani sashi daabun yafi shafanmu.  

"Muna rokon kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya da su gaggauta warware sabanin dake tsakaninsu.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci