OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ambaliyar Ruwa: Sama Da Gidaje 200 Suka Ruguje a Makurdi - SEMA

Ambaliyar Ruwa: Sama Da Gidaje 200 Suka Ruguje a Makurdi - S

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Benue (SEMA) ta ce sama da gidaje 200 ne ambaliyar ruwa ta ruguza. 

Sakataren zartarwa na hukumar a jihar, Dr Emmanuel Shior ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Yayin da yake lura da barnar da ambaliyar ta yi, ya ce jihar ba ta taba shaida irin haka ba a baya. 

Ya ce sassan da abin ya shafa a cikin babban birnin jihar sun hada da: "Naka Road, Achusa Kucha Utebe, Gyado Villa, Rukunin akalai da sassan Nyiman da dai sauran su."

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito, Shior ya kara da cewa, jihar na shirin fadada sansanonin da za a tsugunar da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Makurdi, Guma da Logo.

Ya kara da bayyana cewa sama da mutane 400,000 ne suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren da aka kai kan al'ummomi na baya-bayan nan.

Yayin da yake kokawa kan yadda ake samun karuwar ‘yan gudun hijira a jihar, ya roki gwamnatin tarayya da ta taimaka wa jihar wajen kula da su. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci