OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Tinubu ya nada Gwamna Masari, Wamako a matsayin manyan mashawartan yakin neman zaben sa

2023: Tinubu ya nada Gwamna Masari, Wamako a matsayin manyan

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2023, Bola Ahmed Tinubu ya nada Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a matsayin babban mashawarci kan harkokin mulki .

Sannan ya nada tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Wamakko, Sanata mai ci a matsayin babban mai ba da shawara na musamman.

Kamar yadda aka bayyanawa manema labarai nadin a ranar Lahadi a garin Abuja wanda Mista Tinubu ya sanya hannu, An bayyana cewa duka su biyu za su yi aiki a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Wasikun sun bayyana cewa Masari da Wamakko sun samu gagarumar nasara a siyasa da kuma shugabanci nagari da suka nuna akan mukamin su.

Ga abinda wasikar ta ce: “Muna farin cikin gabatar da wannan wasiƙar don tabbatar da nadin naka a hukumance a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin mulki na gwamnatin Tinubu/Shettima Presidential Campaign Council.

“Wannan nadin ya dace da kai idan aka yi la’akari da irin nasarorin da ka samu a siyasance da kuma kyakkyawan shugabanci da ka nuna a matsayinka na gwamnan jiharka da kuma a matsayinka na dan jam’iyya.

"Muna godiya da kuka shiga kungiyar yakin neman zabenmu, mun san za ku yi iyakacin kokarin ku."

 Mista Tinubu, a cikin wasikar, ya bayyana fatan cewa Mista Masari zai taimakawa jam’iyyar wajen gudanar da yakin neman zabe mai inganci wanda zai kai ga samun nasara a zaben shugaban kasa na 2023. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci