OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

2023: Nan Ba ​​Da Jimawa Ba Zan Bayyana Zaɓina, Cewar Wike

2023: Nan Ba ​​Da Jimawa Ba Zan Bayyana Zaɓina, Cewar W

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi niyyar bayyana zabin sa a cikin 'yan takarar shugaban kasa da zai marawa baya a zaben.

Wike ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da aikin hanyoyin cikin garin Eneka, karamar hukumar Obio/Akpor, jihar Ribas a ranar Litinin.

Ya ce ya san ’yan takarar da ke da kyakkyawar manufa ga Najeriya kuma zai wayar da kan ‘yan kasa su zabe su a lokacin da ya dace.

“Wasu mutane sun shagaltu, suna hada kawunansu kan yadda za su karbi ragamar mulki a Najeriya domin su wawure sauran arziƙin ƙasa," cewar Wike.

"Ina da masaniya kuma a lokacin da ya dace zan gaya muku su waye waɗannan mutanen."

Dangane da taken jam’iyyar adawa ta PDP da ɗan takararta na shugaban kasa na nufin ceto Najeriya, gwamnan Rivers kamar yadda jaridar Vanguard ta tattaro ya ce:

“Ka manta da duk mutanen nan da suke yawo suna cewa suna son ceto Najeriya, ku jira kawai don ganin abin da zai faru a gaba.

“Dukkanmu mu natsu game da abin da ke faruwa a PDP,  A gaskiya, har yanzu babu abin da ya faru, Amma da yardar Allah wani abu zai faru”.

“Ku duba mun maida hankali wajen baiwa al’ummarmu shugabanci na gari.

"Menene shugabanci nagari?  Kyakkyawan shugabanci yana sa jama'a su yi farin ciki.

“Kyakkyawan shugabanci na samar da ababen more rayuwa ga jama’a. 

Kyakkyawan shugabanci ba batun jam’iyya ba ne."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci