OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Zaben 2023: Kungiyoyin Arewa 37 Sun Amince Da Tinubu A Matsayin Shugaban Kasa

Zaben 2023: Kungiyoyin Arewa 37 Sun Amince Da Tinubu A Matsa

APC Chieftain and Presidential Aspirant of the APC, Bola Ahmed Tinubu|

Kungiyar Arewa Organizations Movement for Asiwaju, wata gamayyar kungiyoyi 37 a Arewa, ta amince da jigon APC, Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa a zaben 2023.

Kungiyar ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya fi cancantar tsayawa takarar.

Kodinetan kungiyar, Sanata Abu Ibrahim ne ya bayyana hakan a fadar gwamnatin jihar Katsina yayin wata ziyara da suka kai masa.

Ibrahim ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar APC mai mulki da su mara wa dan takarar su baya a yunkurin sa.

A yayin da yake jaddada cewa Tinubu ya kasance makusancin Arewa musamman Katsina, ya bayyana cewa shine wanda ya sauya jihar Legas a lokacin da yake gwamna.

Gwamna Masari wanda ya yi magana a lokacin da yake maraba da kungiyar ya nuna jin dadinsa kan ziyarar, inda ya kara da cewa Tinubu dan kishin kasa ne.

Ya kuma yi kira ga duk sauran kungiyoyin da ke goyon bayan Tinubu da su hade kan su a matsayin kungiya daya domin samun nasara.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci