OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

YANZU-YANZU: Kungiyoyin SSANU Da NASU Sun Dakatar Da Yajin Aiki

YANZU-YANZU: Kungiyoyin SSANU Da NASU Sun Dakatar Da Yajin A

Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU) da kungiyar ma’aikatan da basa koyarwa (NASU) sun dakatar da yajin aiki.

Rahotanni sun nuna cewa kungiyoyin sun shiga yajin aikin ne a watan Maris, ‘yan makonni bayan kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) sun shiga nasu yajin aikin.

A zantawarsa da wakilin Jaridar Daily Trust a ranar Asabar, Shugaban SSANU, Kwamared Mohammed Haruna Ibrahim ya ce an dakatar da yajin aikin na tsawon watanni biyu.

 Ya ce kungiyoyin sun dauki matakin ne domin baiwa gwamnatin tarayya damar aiwatar da dukkan yarjejeniyoyin da aka cimma.

 “Mun dakatar da yajin aikin na kwanaki 60 kawai.  Wannan kawai don budewa gwamnatin tarayya taga ta cika dukkan yarjejeniyoyin da ta kulla da mu.  

"Za mu koma yajin aikin bayan kwanaki 60 idan gwamnati ta kasa cika alkawuran da ta dauka,” kamar yadda Kwamared Ibrahim ya shaida.

Ya ce dakatar da yajin aikin zai fara aiki ne a ranar Laraba 24 ga watan Agusta.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci