OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

’Yan Takarar Gwamna A PDP Sun Bayyana Matakai Na Warware Rikicin Atiku Da Wike

’Yan Takarar Gwamna A PDP Sun Bayyana Matakai Na Warware R

‘Yan takarar gwamna a  jam’iyyar adawa ta PDP sun bayyana matakin su na karshe na samar da mafita mai dorewa kan takaddamar siyasa tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Abubakar Atiku da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.

‘Yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP za su gana da kwamitin ayyuka na jam’iyyar na kasa domin yanke hukunci nan ba da jimawa ba.

An samu karin bayanai kan ganawar da ake shirin yi da jam'iyyar da kwamitin yayin da daya daga cikin 'yan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, Isa Mohammed Ashiru ya nuna cewa an riga an warware rikicin da ke tsakanin Atiku da Wike.

"Za mu gana da kwamitin ayyuka na kasa don yanke shawara," in ji shi.

Ya kara da cewa su ('yan takarar gwamnan PDP) suna ganawa da kwamitin domin daukar matsaya kan lamarin.

Tun da farko Ashiru ya jagoranci tawagar wasu ‘yan takarar gwamna 16 na jam’iyyar PDP da suka hada da Katsina, Sokoto, Jigawa, domin ganawa da Wike a gidansa dake Rumueprikon a karamar hukumar Obio-Akpor ta jihar Ribas.

‘Yan takarar PDP sun yi kira ga Wike da ya goyi bayan shugabancin Atiku da abokin takararsa, Dokta Ifeanyi Okowa, da kuma shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu.

A taron wanda ya dauki kimanin sa’o’i biyu ana gudanar da shi, Jaridar Vanguard ta samu labarin cewa ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP musamman sun roki Wike da ya yafewa Atiku da Ayu.

Idan za'a tunawa Wike ya yi takun-saka da Atiku bayan faduwa zaben fidda gwani na jam’iyyar a watan Mayu.

Gwamnan jihar Ribas ya fusata da zaben Okowa a matsayin wanda Atiku ya zaba a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci