OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Makonni da suka shude

'Yan Ta'adda Da Dama Sun Bakonci Lahira a Rikicin Da Ya Barke Tsakanin Su a Zamfara

'Yan Ta'adda Da Dama Sun Bakonci Lahira a Rikicin Da Ya Bark

Biyo bayan wata arangama tsakanin wasu gungun ‘yan bindiga da ke hamayya da juna a jihar Zamfara, an kashe mutane da dama ciki har da wasu mashahuran ‘yan bindiga biyu.

Rikicin wanda aka bayyana shi a matsayin rikicin da yafi kowanne ya yi sanadiyar mutuwar manyan ‘yan bindiga, Dullu da Dan Maigari a karamar hukumar Shinkafi ta jihar.

Wasu gungun ‘yan bindigan Bello Turji ne suka kai wa mutanen biyu hari tare da kashe wasu 15 a safiyar ranar Talata.

AllNews ta tattaro cewa bangarorin sun dade suna takun saka tsakanin su. 

An ce an kashe shugaban wani gungun ‘yan fashi kuma yaron Turji mai suna Na-Sanda a yayin arangamar.

Majiyoyi sun bayyana cewa Turji ya yi awon gaba da mutane da dama daga yankin a yayin arangamar amma daga baya ya kashe su.

Wata majiya ta bayyana cewa rikicin ya bar gawarwaki a yankin da suka hada da Dullu da Dan Maigari.

Da yake tabbatar da rahoton, Daily Trust ta kuma ruwaito cewa Bello Turji ya rasa mutanensa da dama amma babu hakikanin adadin mutanen da ya rasa.

A halin da ake ciki an ga yawancin mutanensa da raunukan harbin bindiga.

Sai dai duk kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Shehu Mohammed ya ci tura.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci