OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Sace Wani Fasto A Jihar Filato

'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Sace Wani Fasto A Jihar Filato

Nigerian Police

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da yin garkuwa da Rabaren Bung Dong a unguwar Ganawuri da ke karamar hukumar Riyom a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Alfred Alabo ne ya tabbatar da hakan.

A cewar sa, an sace Rev. Dong ne a daren Lahadi tare da wani mutum mai suna James Mann.

Sai dai Mann wanda kani ne ga Alkalin Alkalan jihar, Mai Shari’a David Mann, ya samu nasarar kubuta da taimakon ‘yan banga a yankin.

Alabo ya kara da cewa tuni rundunar ta tura jami’anta domin gudanar da aikin kame da ceto.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Shugaban kungiyar Atten Youths Movement, Song Moro ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 20.

Moro ya kara da cewa al’ummar yankin sun shaida yadda aka sace mutane hudu kenan a kwanan nan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci