OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

‘Yan Bindiga Sun Sace Jami’an ‘Yan Sanda Da Tsakar Rana A Jihar Ogun

 ‘Yan Bindiga Sun Sace Jami’an ‘Yan Sanda Da Tsakar Ra

Bandita

Wasu ‘yan bindiga sun sace wasu jami'an  ‘yan sanda uku a Wasinmi da ke karamar hukumar Ewekoro a jihar Ogun.

Rahotanni sun nuna cewa an yi awon gaba da jami’an da suka ziyarci jihar Ogun daga shiyya ta 2, Onikan a jihar Legas domin gudanar da bincike, da rana tsaka.

‘Yan bindigar sun yi awon gaba da jami’an karkashin jagorancin Sufeto Oladipo Olayemi da misalin karfe 2:30 na rana.

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda reshen jihar Ewekoro sun kaddamar da farautar wadanda suka yi garkuwa da su.

Kakakin ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da sace jami'an, amma ya ce “Dan sanda daya ne ke hannun ƴan bindigar.

Yayi alƙawarin rundunar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ceto jami'an na ta ba tare da sun samu wani rauni ba.

.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci