OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2 A Garin Udawa Da Ke jihar Kaduna

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 2 A Garin Udawa Da Ke jihar Kadu

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wasu mutane 2 a kauyen Udawa da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna a harin da misalin karfe 8 na daren ranar Lahadi.

Shugaban yankin, Muhammadu Umaru, ya tabbatar wa Jaridar Daily Trust cewa daya daga cikin wanda aka kashe makaho ne.

Ya ce mazauna garin sun fito domin fatattakar ‘yan bindigar tare da goyon bayan jami’an tsaro da ke kusa da su inda suka yi nasarar korar su.

“Wadanda aka kashe sun hada da Sarkin Komo wanda bai dade da dawo wa kauyen ba yayin da dayan makaho ne wanda harsashi ya same shi.

Ya ce matsalar tsaro a yankin ya na matukar damun su, inda ya bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar.

An kasa samun wayan Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar, DSP Mohammed Jalige, a lokacin hada rahoton.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci