OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Yan Bindiga Sun Kai Samame Funtuwa, Sun Sace Mata Da Yara 3 A Katsina

Yan Bindiga Sun Kai Samame Funtuwa, Sun Sace Mata Da Yara 3

Photo Source: PremiumTimes

Biyo bayan wani farmaki da ‘yan bindiga suka kai, an sace wata mata da ‘ya’yan kishiyar ta guda uku a karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina.

An kai harin ne a ranar Talata a gidan wani Shamsuddeen Muhammad Kalgo.

An bayyana cewa wadanda aka yi garkuwa da su din matar Kalgo ne da ‘ya’yan kishiyar ta masu shekaru tsakanin 6 zuwa 12.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, yayan Kalgo ya bayyana wa Jaridar Daily Trust cewa lamarin ya faru ne a lokacin da kanin sa ke tare da matar sa ​​ta farko a wani gida.

Ya bayyana cewa, “Yana da mata biyu kuma kowacce tana zaune a wani gida daban. Wacce aka sace ita ce amarya.

“Sun yi aure kwanan nan, bai kai wata biyar ba, don haka yaran da suke hutu na daya matar ne, a lokacin yaran su hudu ne, amma an yi garkuwa da uku, aka bar karamin cikin su.

Yayin da masu garkuwan suka tuntubi dangin tare da bayanin cewa wadanda aka sace din suna cikin koshin Lafia, babu wata tattaunawa da aka fara domin a sako su.

Sai dai har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa akan lamarin ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci