Wasu 'yan Arewa lokacin da suke gudanar da zanga-zanga a birnin Landan
Wasu Arewa dake zaune a birnin Landan sun gudanar da zanga-zanga don nuna bacin ran su kan rashin tsaron dake kara ta’azzara a Najeriya, musamman Arewacin ta.
Masu zanga-zangar da suka tun karfe 12:00 rana na Alhamis sun ce yadda ake kashe ‘yan Arewa ba tare da shugabanni sun yi wani katabus wajen hana hakan baa bin takaici ne matuka.
Masu Zanga-zangar sun bayyana takaicin su kan yadda ake kashe yan Arewa ba tare da shugabanni sun dau wani kyakkyawan yunƙuri na dakatar da kisan ba.
Cikin wadanda suka jagoranci Zanga-zangar akwai fitaccen lauyan nan Barista Audu Bulama Bukarti da fitaccen dan jarida Ja’afar Ja’afar.
Masu zanga-zangar sun zargi shugaban kasa, Muhammadu Buhari a matsayin wanda baya daukar shawarwarin kan yadda za’a samar da tsaron.
Sun bukaci shugaban kasar da wadanda nauyin magance matsalar ya rataya a wuyan su da su gaggauta daukar matakan sace da kuma kashe ‘yan Arewar da a kullum.
0 Tsokaci