OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Yajin aikin ASUU: Ba a kafa mu don yakar kowa ba – CONUA

Yajin aikin ASUU: Ba a kafa mu don yakar kowa ba – CONUA

Dr Niyi Sunmonu

Shugaban sabuwar kungiyar ‘Congress of Nigeria University Academics’ (CONUA) Dr Niyi Sunmonu, ya bayyana cewa ba wai an kafa ta ne don nuna gaba ko fada da kowa ba.

 

 Rijistar hukumar ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar nan, a daidai lokacin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke ci gaba da yajin aikin.

 

 Da yake magana a wata hira da jaridar Punch, Dr Niyi  ya ce: "Ba a kafa CONUA ba saboda tana son nuna adawa ko kuma tana son fada da kowa; a'a, Larura ce ta sanya aka kafa kungiyar 

 

 “mun zama tamkar saniyar ware a waccan kungiyar shi yasa muka ga dacewar kafa wata kungiya ta daban, Amman duk da hakan muna sa ran yin hadin gwiwa da dukkan kungiyoyin malaman jami'o'i 

 

 Don haka, mu bama fada da kowa. Kuma zai zama tamkar rashin da'a ne in fara sukar manufofi da matakan da wasu kungiyoyin suka dauka"

 

 Dr Niyi ya Kara da cewar a kullum- fatan sa shine a Warware matsalar dake tsakanin ASUU  da gwamnatin tarayya ta yadda CONUA zata mu samu yanayi mai kyau da zai taimaka wajen yin aiki tare domin cigaban ilimi a kasar nan.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci