OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sojoji Sun Ceto Basaraken Filato Da Direban Sa Daga Masu Garkuwa Da Mutane

Sojoji Sun Ceto Basaraken Filato Da Direban Sa Daga Masu Gar

Dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven’ a jihar Filato sun ceto sarkin kauyen Pinau, Dadda’u Ahmad da ke karamar hukumar Wase a jihar.

Kakakin rundunar, Ishaku Takwa ne ya bayyana hakan.

A cewar Takwa, tuni aka hada basaraken da iyalansa.

Ku tuna cewa an sace sarkin ne tare da direbans a da sanyin safiyar Talata.

Wani mazaunin garin, Ubale Pinau ya shaida wa Daily Nigerian cewa sojojin sun ceto mutanen ne a lokacin da suka samu labarin sace su.

A yayin aikin, babura uku da bindigogi biyu ne aka kwato. 

Wani dan banga a unguwar mai suna Nazifi Abubakar ya ce an kai harin ne tare da mutanen su.

A cewar sa: “Ina tare da sojoji a yayin aikin ceton.

“Sojoji da wasu ’yan bangan unguwar ne suka dawo da basaraken kauyen, wadanda suka bi sahun masu garkuwa da mutanen zuwa daji.

“Kowa yana farin ciki a ƙauyen yanzu. 

"An yi musayar wuta tsakanin sojoji da maharan kafin a ceto wadanda abin ya shafa."

Ya Kuma yaba wa dakarun yayin da yake addu’ar Allah ya kara musu nasara.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci