OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Shugaban kungiyar ASUU ya bayyana cewa a shirye suke su janye yajin aiki

Shugaban kungiyar ASUU ya bayyana cewa a shirye suke su jany

Shugaban kungiyar malaman Jami'o'i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa indai har gwamnati ta yarda da kudurinsu su kuma a shirye suke su janye yajin aiki.

“Dukkan abubuwan da ke faruwa mun bai wa gwamnati zabi akan iya abunda zamu iya karba, amma sukayi watsi da kudurin mu basu ce komai ba .

Mun nemi a sake farfado da kudurorin mu da kuma batun alawus-alawus da  sauran batutuwa da muka tattauna.

"Mun yi yarjejeniyar cewa mun amince su sanya hannu wannan abu ne mai sauki, abune da bai wuce a yi shi rana daya ba.

“Akan UTAS da IPPIS, mun ce su fitar da rahoton gwajin da suka yi, mu kuma zamu duba yiwuwar komai kamar yadda aka tsayar da yarjejeniya.

“Mun gaya musu mafi karancin abin da muke so wanda da haka ne zamu sauko,wannan abu ne da ba zai wuce a aiwatar da shi a kwana daya ba,” inji mista Osodeke.

 “Idan har gwamnati na son kasar nan, tana kuma son dalibai da iyayen dalibai , to rana daya ya ishemu mu zauna akan teburi mu warware wadannan matsaloli.

In ba a manta ba kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki ne tun a ranar 14 ga watan Fabrairu, wanda suka shafe tsawon watanni bakwai jami'o'i kasar nan na rufe.

A kwanakin baya an ji cewar gwamnatin tarayya ta maka kungiyar ASUU a kotu domin kawo karshen yajin aikin da suke yi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci