OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Shugaban Jami'ar Tarayya Ta Dutse Ya Bayyana Fatan Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU Kwanan Nan

Shugaban Jami'ar Tarayya Ta Dutse Ya Bayyana Fatan Kawo Ƙar

Masu ruwa da tsaki na ta kiraye kirayen kawo ƙarshen yajin aikin da ASUU ta fara tun 14 ga Fabarairun 2022.

Shugaban Jami’ar tarayya ta Dutse, FUD, Farfesa Abdulkarim Sabo yace gwamnatin tarayya ta gayyaci shugabannin jami’o’in ƙasar nan ne a matsayin ma’aikatan ta, ba wai ‘yan kungiyar malaman jami’o’I ta kasa, ASUU ba, inda ya bayyana fatan kawo ƙarshen yajin aikin nan ba da jimawa ba.

A jiya Laraba ne hukumar gudanar da jami’o’I ta kasa, NUC ta aikewa da shugabannin jami’o’in sanarwar su halarci wani taro da zai gudana ranar shida ga watan Satumbar da muke ciki, a wani yunkuri na kawo daidaito tsakanin kungiyar ASUU ga gwamnatin tarayya.

Batun yajin aikin da kungiyar ASUU ta fara tun 14 ga watan Fabarairu ya fara damun iyayen yara, da dalibai da ma wasu malaman dake koyarwa a wadannan jami’o’I, musamman ganin yadda gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU suka kasa cimma matsaya tsawon wannan lokaci.

Yanzu haka an fara samun wasu jami’o’in jihohi sun fara janye jikin su daya bayan daya daga tafiyar kungiyar ta ASUU wanda wala All… ba zai rasa nasaba da barazanar da gwamnatocin jihohin su ke musu.

Duk kiraye kirayen masu ruwa da tsaki da shugabanni a matakai daban daban ya gaza kawo karshen yajin aiki.

Kan haka ne ma hukumar dake kula da jami’o’I ta kasa, NUC ta bukaci dukkan shugabannin jami’o’in dasu halarci wani taro a ranar 6 ga watan da muke ciki.

Shugaban jami’ar tarayya ta FUD ya ce, ana sa ran bayar da shawarwarin da zasu kawo karshen yajin aikin da yaki ci yaki cinyewa a wannan zaman.

Kan batun tsame jiki daga ASUU, da komawa makarantu da wasu jami’o’in ke yi kuma, Farfesa Abdulkarim Sabo ya danganta hakan da dadewar da aka yi ana yajin aikin, da kuma yadda wasu jihohin ke ci gaba da biyan malaman duk da yajin aikin da suke yi.

Ya jaddada fatan sun a ganin yajin aikin da yanzu kungiyar ASUU ta aiyana da na sai baba ta gani zai zo karshe nan kusa domin ci gaban ilimi a Najeriya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci