OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Sarakunan Arewa Da Gwamnoni Sun Goyi Bayan Ƴan Sandan Jihohi

Sarakunan Arewa Da Gwamnoni Sun Goyi Bayan Ƴan Sandan Jihoh

Simon Bako Lalong

A yayin da ake fama da matsalar tsaro a Najeriya, gwamnonin Arewa 19 da daukacin sarakunan gargajiya na yankin na goyon bayan rundunar ‘yan sandan jihohi.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron kungiyar gwamnonin Arewa (NGF) da majalisar sarakunan Arewa (NTRC) da suka gudanar a daren Litinin a Abuja.

Amincewar ta biyo bayan tuntubar juna a tsanake domin a cewarsu ta haka ne kawai za a iya magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin da ma kasa baki daya.

Taron da shugabannin Arewa suka yi mai taken "Bita kan yanayin tsaro a Arewa da sauran abubuwan da suka shafi ci gabanta da ci gaban yankin."

Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong;  Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya;  Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari;  Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Sauran sun hada da gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu;  Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum;  Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello;  Gwamnan jihar Taraba, Darius Dickson Ishaku;  da mataimakan gwamnonin jihohin Adamawa, Benue, Nasarawa da Jigawa.

Yayin da Sarakunan Gargajiya da suka halarta sun hada da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III;  Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi;  Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero;  Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli;  Sarkin Fika, Alhaji Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa;  Sarkin Lafia, Justice Sidi Bage Muhammad.

Daga ciki akwai Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad, Sarkin Gumi, Justice Lawal Hassan Gumi;  Attah Igala, Mathew Opaluwa;  Ochi’Idoma, Fasto John Elaigwu;  da Aku Uka na Wukari, da Dattijo Manu Ishaku Adda Ali, da sauransu.

Shugaban kungiyar  gwamnonin, Simon Lalong ya ce taron ya yi nazari kan yanayin tsaro a Arewa da sauran al’amura da suka shafi ci gabanta.

Sun kuma kuduri aniyar goyon bayan yiwa kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 gyara domin a dauki nauyin kafa ‘yan sandan jihohi, inji rahoton Daily Trust.

Sanarwar ta ce "Wannan zai magance kalubalen tsaro yadda ya kamata."

 “Masu rajin goyon bayan  ‘yan sandan jihohi na cewa zai zama mawuyaci ace ‘yan sandan kasa mai girman Najeriya ana juyasu daga Abuja, babban birnin tarayya.

Taron ya kuma nuna rashin jin dadinsa dangane da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi, wanda suke ganin ya fi tasiri a yankin kasancewar yawancin daliban Arewa na zuwa jami’o’in gwamnati.

Sanarwar ta kara da cewa, "Saboda haka, ta yi kira ga ASUU da ta hada kai da gwamnatin tarayya wajen warware rikicin."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci