OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ruwan Sama Haɗe Da Ƙanƙara Ya Lalata Gonaki Da Gidaje A Ƙauyukan Katsina

Ruwan Sama Haɗe Da Ƙanƙara Ya Lalata Gonaki Da Gidaje A �

Photo Source: Legit Hausa

Biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi a Katsina wanda ya haifar da ƙanƙara ta lalata gonaki da gidaje a unguwannin Dutsen-Kura/Kanya da Gozaki a karamar hukumar Kafur ta jihar.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Malam Abdullahi Gozaki, wani mazaunin garin Gozaki ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa a yankin babu wanda ya taba ganin faruwar irin wannan lamari.

Yace hakan ya lalata filayen noma da rufin gidaje da gilashin mota sakamakon guguwar ƙanƙara da ta dauki tsawon mintuna.

Sai dai ya lissafta al’ummomin da abin ya shafa kamar su Gidan Danwada, Gidan Sabo, Kabalawa, Unguwar Tsamiya, Dandabo, Unguwar Maigarma, Unguwar Wanzamai da Unguwar Fulani.

Da yake tsokaci, shugaban karamar hukumar Kafur, Alhaji Garba Kanya, ya ce dusar ƙanƙarar ta lalata gonaki kusan 350 a cikin al’ummomi da dama wanda hakan ya tilastawa mutane barin gidajensu.

Yayin da yake tabbatar da lamarin, yace ƙanƙaran ya lalata amfanin gona da dama na miliyoyin naira da suka hada da masara, gero, shinkafa, waken soya, da sauransu.

Ya kara da cewa, a wasu gonakin, ana shirin girbe shinkafa ne bayan masu gonakin sun kammala kusan dukkan ayyukan gonan.

Ya bayyana cewa an sanar da hukumomin da abin ya shafa kamar Hukumar Noma da Raya Karkara ta Jihar Katsina (KTARDA) da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) kuma sun ɗauki bayanai akan irin barnar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci