OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rundunar Yan Sandan Kano Ta Kama Matashin Da Ya Buge Wani Yayin Kilisa

Rundunar Yan Sandan Kano Ta Kama Matashin Da Ya Buge Wani Ya

Nigerian Police force

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Aminu Kabiru mai shekaru 18, da ake zargi da bige wani mai suna Abdulhadi Sammani mai shekaru 20 da doki.

Kakakin rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da kama matashin bayan wasu matasa sun gudanar da kilisa da dokuna a unguwar Gadan Kaya.

Yace bayan faruwar lamarin sun kai wanda aka buge da dokin asibitin Murtala Muhammad inda likita ya tabbatar rasuwar sa, wanda hakan ya sa suka kama mutum daya da wani doki domin gudanar da bincike.

Ko a baya, rundunar yan sandan jihar Kano ta haramta yin kilisa ba tare da neman izini ba, bayan da aka yawaita samun rahotannin take mutane da dokuna yayin gudanar da ita.

Amma wannan umarni bai hana matasa a sassa daban-daban a jihar hada kilisa ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci