OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Rahama Sadau Ta Nisanta Kanta Da fitowa cikin 'yan kwamitin takarar Tinubu

Rahama Sadau Ta Nisanta Kanta Da fitowa cikin 'yan kwamitin

 Fitacciyar jarumar kannywood Rahama Sadau, ta nisanta kanta daga jerin manyan matan da aka fitar da sunayen sun dan yin kamfen din Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a zaben shugaban kasa mai zuwa.

A cikin takardar yakin neman zabe mai shafuka 70, ‘yan wasan Nollywood da na Kannywood kusan su 33 ne aka shigar da sunayen su don yakin neman zaben Tinubu.

Yayin da take nisanta kanta daga jerin sunayen da aka fitar a ranar Asabar, jarumar ta bayyana labarin a matsayin ‘karya.

Da take bayyanawa a shafin ta na Twitter,ta rubuta, cewa:"WANNAN KARYA NE… BAN SAN WANNAN BA… BAN SAN YADDA AKA YI SUNANA YA FITO BA.

A ranar murnar samun ‘yancin kai, jam’iyyar All Progressives Congress ta sanar da jerin sunayen kamfen na mata wanda uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari; Sanata Oluremi Tinubu da Hajiya Nana, uwargidan dan takarar mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne suka jagoranci kwamitin.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci