OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Adams Oshiomhole Ya Zargi Yan Siyasa Da Bayar Da Gudunmawa Wajen Rikicin Zabe

Adams Oshiomhole Ya Zargi Yan Siyasa Da Bayar Da Gudunmawa W

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,Adams Oshiomhole ya ce shugabannin siyasa na ba da gudunmawa wajen tashe-tashen hankula da ake yi a lokutan zabe.

Tsohon gwamnan jihar Edo ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata yayin tattaunawar zabukan ‘yan kasa da kungiyar YIAGA Africa da hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) tare da hadin gwiwar Channels TV suka shirya.

Oshiomhole ya ce irin  makaman da masu kawo tarzoma ke amfani da su ba a samun su cikin sauki.

Ya ce, “Lokacin da nake gwamna kuma, ina mai tabbatar muku da  hakan, za ku iya tambayar (tsohon) shugaban kasa Goodluck Jonathan, na taba yin wata magana a wani taro a Villa cewa, a wasu lokutan gwamnonin suna bayar da gudunmawa wajen tashe-tashen hankula a zabe saboda AK-47 ba arha ne da ita ba,  kamar siyan  kosai 

“Kuma idan ka ga samari da yawa da ba su da aikin yi suna rike da AK-47, to a ina suka samu su? Don haka shugabancin siyasa yana da nauyi, ya kamata mu dauki wannan nauyi.

“Idan masu zabe 500 suka zabi yin tashin hankali, ‘yan sanda nawa kuke son turawa? Mu yarda da cewa a matsayinmu na jam’iyyun siyasa, mun yarda cewa a yayin yakin neman zabe, a kowane lokaci, dole ne mu jaddada cewa wannan zabe ya shafi ‘yancin zabar ta ayine  ne kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne tsari, ba ma sakamakonsa ba.

“Yakamata mu dawo mu gayawa  shugabanninmu cewa dole ne su yi kira ga mutanensu da kada suyi rikici a Lokutan zabe. Ina jaddada cewa dukkanmu a nan akwai hakki Akanmu. Najeriya tana da yawan. jam'iyyun siyasa."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci