OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Majalisar Wakilai Za Ta Tafi Yajin Aiki Saboda Tabarbarewar Tsaro

Majalisar Wakilai  Za Ta Tafi Yajin Aiki Saboda Tabarbarewar

‘Yan Majalisar Kasar nan sun ce za zu iya tafiya yajin aiki saboda ci gaba da Kamari da rashin tsaro ke yi a kasar nan,

A ‘yan kwanakin nan, yan ta’adda sun kara kaimi wajen kai hare-hare babu kakkautawa wasu jihohin kasar nan ciki gar da Kaduna, Katsina, Niger, Zamfara da sauran su.

Da yake bayani, dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Fagge daga Jihar Kano, Aminu Sulaiman Goro a Alhamis din nan ya sanar da manema labarai cewa suna samun labarin dukkan hare-haren da ‘yan ta’addan ke kaiwa.

Yace yadda maharani ke sacewa tare da kashe al’umma, musamman a Arewacin Kasar nan, abin tashin hankali ne matuka.

Sai dai ya ce harin bam din da ‘yan bindiga suka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya munana, saboda tuni aka hana mutane bin tituna saboda gudun kai musu hari.

”Wannan ya nuna cewa an kama sama an kama kasa gashi nan dai, to ban san me suke so su yi ba.

“Mu a matsayinmu na ‘yan majalisa mun ga cewa dukkan abin da gwamnati ta nema na harkar kasafin kudi ko doka, ba mu taba bata lokaci ba muna amincewa, to amma kullum masifar nan kara ta’azzara take.

“Muna ganin kamar jama’ar da muke wakilta sun fara gajiya, ba wai iya gwamnati ba, har mu kanmu.

“Duk abin da za mu yi mun yi don ganin an inganta harkar tsaro, to amma kullum jiya a yau, don haka muka ga cewa lallai-lallai ya kamata mu yi wani abu daban, mu rufe majalisa mu tashi.”

Ya kara da cewa, “Za mu tashi har sai jami’an tsaro sun zo sun gaya mana mene ne ya ke faruwa? kuma menene za su yi?, sannan idan sun gaza me suke bukatar mu yi musu?”.

Goro ya ce a wasu lokutan suna da masaniyar abubuwan da gwamnati ke yi amma a wasu lokutan ba su san me take aikatawa ba.

“Don haka idan mu ma za mu bi sahun ASUU ne, mu ma mu shiga yajin aiki, gara mu rufe mu tafi har sai an tabbatar mana da cewa jama’ar da suka turo mu wakilci, lafiyarsu da dukiyarsu da kuma rayukansu za su zamanto cewa an kare su.”

Kwanaki hudu da suka gaba ne dai ‘yan bindiga suka kai hari kan jirgin kasan Kaduna, inda suka kashe wasu daga mayafiyan, tare da sace wasu.

Wasu da dama kuma sun samu raunuka iri-iri.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci