OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Naɗin Kabiru Muhammad A Matsayin Kwamishina

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Naɗin Kabiru Muhammad A

Majalisar dokokin jihar Kano

Majalisar dokokin Kano ta amince da nadin Kabiru Muhammad Tarauni a matsayin kwamishina kuma dan majalisar zartaswa na jihar Kano.

Majalisar ta amince da shine a zamanta na yau Litinin karkashin shugabanta Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Gamduje, ne ya aike sa sunan sa ga majalisar dokokin domin tangancewa tare da amincewa dashi a matsayin kwamishina.

A yanzu dai shine mutum na goma sha daya da majalisar ta amince dasu domin nada su a matsayin kwamishinoni da zasu maye gurbin wadanda suka ajiye aiki don yin takara a zaben badi dake tafe.

Kafin amincewa dashi Kabiru Muhammad Tarauni, ya taba zama dan majalisar dokokin Kano karo biyu daga shekarar 2003 zuwa 2011.

Yayin zaman sa a majalisar ya rike mukamin bulaliyar majalisa.

 

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci