OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mahalarta Taron Sauyin Sun Bukaci Sanya Manhajar Sauyin Yanayi A Jadawalin Koyarwa

Mahalarta Taron Sauyin Sun Bukaci Sanya Manhajar Sauyin Yana

Mahalarta taron kasa kan sauyin yanayi sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta sanya manhajar sauyin yanayi a cikin jeren manhajojin ilimin kasar nan.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da babban darakta na Hukumar Kula da Kare Hakkin Jama’a, Akinbode Oluwafemi, ya sanya wa hannu a karshen taron kasa da aka yi na kwanaki biyu a Abuja.

Mahalarta taron sun ce sanya manhajar zai taimaka wajen sanyawa matasa sha’awa tare da son kare muhallin da suke ciki.

Sai dai da yake tsokaci kan wannan batu shugaban sashen tsangayar ilimi na jami’ar Bayero dake Kano, Dr. Ali Idris yace saka irin wadannan manhajoji a cikin jerin manhajar ilimin kasar nan, za'a iya fuskantar kalubale sosai.

A cewar sa, yanzu haka akwai cunkushewar manhajojin, kuma haka ka iya sawa a gaza aiwatar da wanda ya dace.

Yace yanzu haka abubuwan da ake koyarwa a makarantu da yawa, kuka sanya sabon darasi zai kawo cunkoso cikin abubuwan da ake koyarwa.

Dumamar yanayi, ɗaya ne daga matsalolin da suka addabi duniya baki ɗaya, da alhakin yanzu ke kawo matsalolin yanayi da dama kamar ambaliyar ruwa da sauran su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci