OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Mafi Yawan Hatsari Jiragen Ruwa Sakacin Al'umma Ne Sila - NIWA

Mafi Yawan Hatsari Jiragen Ruwa Sakacin Al'umma Ne Sila - NI

Manajan hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa a jihar Legas (NIWA) Injiniya Sarat Braimah ta ce rashin samun horon da ya dace daga masu aikin jiragen ruwa ne ke haddasa mafi yawan hatsarin jiragen ruwa a kasar nan.

Da take jawabi a yayin gabatar da takardar shedar tukin jirgin ruwan da hukumar NIWA ta baiwa jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA Engr Sarat Braimah, ta ce akasarin lokuta da zarar mutane sun samu lasisin tukin jirgin to gani yake zai iya tuka kwale-kwale a dukkan wani  ruwa na cikin kasar nan.

Kamfanin Metropolitan Waterways Concepts Limited ne ya gudanar da horon tukin jirgin tare da tallafi daga Hukumar Biritaniya a jihar Legas.

Injiniya Braimah tace "mafi yawancin alumar da suke zuwa NIMA neman lasisi sukan yi tunkahon tun suna yara suke shiga ruwa ko kuma mahaifinsu ma’aikacin jirgin ruwa ne kuma sun sami ilimi a wurinsa.Ba su san cewa ya wuce haka ba kamar tukin mota ne.Akwai ka'idoji da kuma hanyoyin da ya kamata a bi"

A jawabin ta wakiliyar shugaban Hukumar Biritaniya a Legas, Marie Maxwell ta ce horon wani bangare ne na gudummawar su ga Hukumar ta NDLEA ke bayarwa wajen yaki da miyagun kwayoyi a Najeriya.

Ta kuma kara da cewar "muna tallafawa aikin gina tashar ruwa da filin jirgin sama domin mun gamsu da gagarumar nasarar da hukumar NDLEA ta samu a yakin da take da miyagun kwayoyi, wannan horo na wani bangare ne na shirye-shiryen shekaru uku na ayyukan bunkasa bankado miyagun kwayoyin domin rage barazanar safari miyagun kwayoyi a cikin ruwan Najeriya. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci