OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Katsina: 'Yan Sanda Sun Kashe 'yan Ta'adda Da Kama Wani Mai Ba Da Labaran Sirri

Katsina: 'Yan Sanda Sun Kashe 'yan Ta'adda Da Kama Wani Mai

Photo Source: Legit Hausa

Rundunar 'yan sanda sun kashe wani dan ta’adda da safiyar Lahadi a kauyen Unguwar Maizuma da ke karamar hukumar Danja a jihar Katsina.

Yayin da kuma suka kama wani mutum da ake zargin yana baiwa ‘yan ta’adda bayanan sirri a kauyen, cewar Jaridar Punch.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan sandan sun mamaye wani wuri mai duhu da ake kyautata zaton maboyar ‘yan ta’adda ce a kauyen da safe bayan wani rahoton sirri da aka samu, wanda ya yi sanadin mutuwar dan ta’addan tare da cafke mai ba da labarin.

Photo Source: Legit Hausa

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayar da karin bayani: “A ranar 20 ga watan Agusta, 2022, da misalin karfe 7:30 na safe, bisa samun sahihan bayanan da aka samu cewa an ga ‘yan ta’adda a kauyen Maizuma Danja, Karamar hukumar ta jihar Katsina, DPO Danja ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa yankin inda suka yi artabu da ‘yan bindigar.

“Rundunar ta samu nasarar fatattakar ‘yan ta’addan tare da kashe daya daga cikinsu.  

"A yayin binciken maboyar, an gano abubuwa kamar haka: bindigar da aka kera a cikin gida;  kakin soja;  adduna da wuƙa;  kwalabe 100;  wasu busassun ganyen da ake zargin wiwi ne,  Babura biyu Boxer;  batirin mota guda uku;  injin dinki daya; USB waya biyu, da abun dafa abinci Silinda gas.

“An kuma kama wani da ake zargin mai baiwa ‘yan ta’addan bayanai ne.  An yi zargin cewa shugaban kungiyar 'yan ta'addan, Sule Dawa, ya tsere da mummunan harbin bindiga.

"Rundunar ta na kokarin kama shugaban kungiyar da sauran mambobin kungiyar."

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Idrisu Dauda, ​​ya yaba da kokarin da jami’an suka yi na dakile ‘yan ta’addan, ya kuma umarce su da su ci gaba da tafiya har sai an magance duk wani nau’in laifi da aikata laifuka.

Kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai a yakin da ake yi na yaki da ta’addanci a jihar.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci