OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Ina Tausaya Wa Shekarau Daya Koma PDP, Inji Buba Galadima

Ina Tausaya Wa Shekarau Daya Koma PDP, Inji Buba Galadima

Buba Galadima| Photo Source: The Niche

Wani jigon jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) Buba Galadima yace yana tausayin Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau da ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Galadima na mayar da martani ne kan ficewar Shekarau daga jam’iyyar NNPP a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya ce ya ji tausayin Sanatan mai ci.

Ya ce mafi yawan magoya bayansa za su ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar domin su shaida nasarar da ta samu a zabe mai zuwa.

“Mun riga mun yi tsammanin faruwar hakan, ina tausaya masa da wannan bijirewar domin ya rasa hanya.

“Kodayaushe yana ikirarin rashin adalci a jam’iyyar da ya koma, ina tabbatar muku a wannan ficewar da aka yi kwanan nan, kashi 90 na magoya bayansa ba za su bi shi ba, za su ci gaba da zama a NNPP.

“Na ce maka babu wata jam’iyya da ke son rasa ko da kuri’a daya domin jam’iyya za ta iya lashe zaben shugaban kasa da kuri’a kuma Shekarau yana da kuri’u sama da daya.

"Ba burinmu ba ne ya bar mu amma tunda ya yanke shawara ku kyale shi, ko da mun ci zabe, ina gaya muku Shekarau ne matsalarmu."

Ya ce jam’iyyar za ta rubuta wa INEC madadin Shekarau a matsayin dan takarar Sanata na Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP a zabe mai zuwa, inji rahoton Daily Trust.

Galadima ya ce babu daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa da ke da kashi daya bisa hudu na magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a Arewa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci