OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

IGP Ya Ba Da Umarnin Bincike Kan Shiga Gidan Mai Shari'a Odili

IGP Ya Ba Da Umarnin Bincike Kan Shiga Gidan Mai Shari'a Odi

IGP Usman Alkali Baba| Hoto Daga: NaijaNews

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Baba, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan harin da aka kai gidan mai shari’a, Mary Odili na Kotun Koli a Abuja.

 

A ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba, 2021, jami’an tsaro dauke da makamai da ake zargin ‘yan Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ne ko kuma Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS) ne ta kai farmaki gidan Mai Shari'ar.

Hakan dai bai cimma riba ba don jami'an tsaro da ke kula da gidan basu bari an shiga ba.

Daga baya kuma hukumomin EFCC da DSS sun musanta zargin tare da wanke hannayen su daga lamarin.

Mai magana da yawun rundunar 'yansandan ta kasa, CP Frank Mba, ya ce shugabancin rundunar ba ta da masaniya, kuma ba a kowane lokaci IGP ya umarci jami'an 'yan sanda su gudanar da irin wannan aiki ba.

"Saboda haka, IGP ya umarci Hukumar Leken Asiri ta Rundunar (FIB) da ta gudanar da bincike na gaskiya game da lamarin," in ji Mba.

Ya kuma tabbatar da aniyar rundunar na tabbatar da kula da tsaron ‘yan majalisar shari’a da ‘yan Najeriya baki daya.

Ya kuma yi kira da a kwantar da hankula, inda ya yi alkawarin cewa rundunar za ta yi duk mai yiwuwa wajen bankado masu aikata wannan aika-aika da kuma nufin gurfanar da duk wadanda ake tuhuma a gaban kotu.

A halin da ake ciki, IGP ya umurci kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya (FCT) Abuja da ya karfafa tsaro a kewayen tituna da gidan Justice Odili domin tabbatar da tsaronta da kuma hana sake afkuwar lamarin.

 

IGP din ya ba da tabbacin cewa za a bayyana cikakken bayanan binciken da ‘yan sandan ke yi bayan kammala bincike.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci