OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Hukumar Kula Da Asibitocin Kano Kano Ta Horas Da Ma'aikatan Jinya

Hukumar Kula Da Asibitocin Kano Kano Ta Horas Da Ma'aikatan

Hukumar kula da asibitoci ta Kano, tace zata rubanya kokarin da take na karawa ma’aikatan asibitocin jihar nan dake karkashin ta kwarewar aiki da samar da kayan zamani don inganta lafiyar al’umar jihar nan.

Babban Daraktan Hukumar, Dr. Nasiru Alhassan Kabo ne ya bayyana haka yayin horar da ma’aikatan jinya na shiyya shiyya da mataimakan su, da ya gudana a asibitin yara na Isyaka Rabi’u a wani yunkuri na kara musu kwarewar aiki.

Dr. Kabo yace suna ci gaba da kokarin tabbatar da ma’aikatan sun samu sabbin dabarun zamani domin aiki yadda ya kamata musamman a manyan asibitocin dake jihar nan.

Ya jaddada cewa bukatar da ke da akwai na sake horar da ma’aikatan lafiya lokaci zuwa lokaci domin tafiya da zamani.
Dakta Kabo ya umarci ma’aikatan jinyar da su zamo masu lura da marasa lafiya cikin girmamawa da lalama domin inganta aikin su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci