OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin Kano Ta Aikewa Da Majalisa Sunayen Kwamishinoni Takwas

Gwamnatin Kano Ta Aikewa Da Majalisa Sunayen Kwamishinoni Ta

Gwamnatin jihar Kano ta aike wa da majalisar dokoki jerin sunayen mutum takwas da take so sumaye gurbin tsaffin kwamishinoni da suka aiki domin yin takara  a kakar zabe mai zuwa.

Shugaban masu rinjayi na majalisar, Labaran Abdul Madari a yayin ganawa da yan jarida ya tabbatar da cewa, gwamnatin Kano ta turo da jerin sunayen mutune takwas da take so a tantance.

Madari ya kara da cewa, gwamnati ta turo da sunayen domin samar da sabbin kwamishinoni da za su cigaba da jan ragamar ma'aikatu a fadin jihar, tare da tabbatar da tafiyar da ayyuka yadda ya kamata.

Jerin sunayen mutum takwas da gwamnatin Kano ta turawa zauren majalisar dokokin domin tantance su a matsayin kwamishinoni a jihar Kanon dai ya hada: 

Alh. Ibrahim Dan'Azumi, Alh. Abdulhamid Abdullahi Liman, Haj. Lamin Sani Zawuya, Alh. Ya'u Abdullahi  Yan Shana, Hon. Garba Yusuf Abubakar, Dr. Yusuf Jibrin, Alha. Adamu Abdul Fanda Hadi da Alh. Sani Kausaini. 

Zauren majalisar dokokin kuma ya umarci mutane takwas din sunan su ke kunshe a takaddar da gwamnatin jihar Kano ta aiko gabatan da su hallara a gabanta a ranar ita yau, 22 ga watan Agustan na shekarar 2022 don tantance su.

 

 

LA/HAM

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci