OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Rahoton Cewa ‘Yan Bindiga Sun Hanyar Kaduna-Abuja

Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Rahoton Cewa ‘Yan Bindiga Sun

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i| Hoto Daga: BBC

Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta rahoton cewa wasu ‘yan bindiga sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Alhamis.

Ku tuna cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana a shafin sa na Twitter ranar Alhamis cewa ‘yan bindiga sun tare hanya da rana.

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, ya ce,“Yanzun nan ne na samu kira mai daga hankali cewa ‘yan bindiga da dama sun sake tare hanyar Kaduna zuwa Abuja da ranan yau. Matafiya suna komawa baya cikin gaggawa.”

Sai dai gwamnatin jihar Kaduna ta bakin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya karyata rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai na cewa, “Cikin cece-kuce da ake ta yadawa, kuma wasu masu sha’awar shafukan sada zumunta ne da kuma son mummunar labari suka bayyana shi.

Aruwan ya ci gaba da bayanin cewa, biyo bayan wuta da jami’an tsaro suka bayar, ‘yan bindigar na tserewa harbin sojoji ne a lokacin da aka hango su a garin Kasarami da ke hanyar.

Haka kuma sojojin sun yi aiki da rahoton sirri da suka samu sannan suka far ma 'yan bindigan.

Aruwan ya kara da cewa, "Gwamnatin jihar Kaduna za ta sanar da jama'a idan aka samu karin bayani."

Ya ci gaba da cewa, duk da cewa gwamnati ba ta musanta cewa jihar na fama da kalubalen tsaro ba, za ta ci gaba da yin aiki tukuru da hukumomin da abin ya shafa domin kawo karshen matsalolin tsaro.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci